Shekarar musulunci tamkar ta miladiya ta kumshi wata goma sha biyu, farawa daga Muharram zuwa Zulhijja.
Kowace shekara malamai da kungiyoyi na musulunci sukan himmatu wajen fadakar da jama'a kan tasirin ta, da kuma bukatar musulmi su kula da amfani da ita.
Wani bincike da VOA ta yi a Sakkwato ya nuna jama'ar basu kulawa da amfani da shekarar musulunci yadda ya kamata.
Duk da karancin kulawa da kalandar musulunci ke samu daga wasu musulmi, malamai sun nace akan cewa tana da tasiri sosai ga musulmin.
Dokta Ibrahim Liman Sifawa, malamin addinin musulunci a Najeriya ya ce duk wani aiki na musulunci da sauran mu'amala ta jama'a suna rataya ne ga kidayar kalandar musulunci.
Muhammad Lawal Maidoki jagora ne a kungiyoyin da ke fafatuka wajen kula da lamurran addinin musulunci a Najeriya, ya ce ya kamata jama'a su farka su rika amfani da kidayar kwanaki na kalandar musulunci tamkar yadda ake yi a lokutan baya.
Yanzu dai shekarar musulunci ta 1444 ta wuce an shigo shekara ta 1445AH, malamai na karfafa gwiwar musulmi da su yi nazarin ayukkan da suka gudanar a shekarar da ta wuce da zummar kara azama wajen aikata wasu kyawawa da nisantar munanan ayukka.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5