Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed ya kira wani taron majalisar dokokin kasar na bazata ranar Litinin 30 ga watan Nuwamba, yayin da ake ci gaba da rikici a yankin Tigray da ke arewacin kasar.
Da yammacin ranar Lahadi, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, shugaban dakarun yankin Tigray na People's Liberation Front (TPLF), Debretsion Gebremichael a wani sakon wayar salula da ya aika wa kamfanin dillancin labaran, ya yi ikirari cewa sojojin Tigray, sun harbo wani jirgin Habasha kuma sun kwace wani gari daga sojojin gwamnatin tarayyar kasar.
Babu wani martani nan da nan game da wannan ikirarin daga gwamnati ko sojojin kasar.
A wani labarin makamancin wannan, ofishin jakadancin Amurka a Eritrea ya ya ce, an ji karar wasu fashe-fashe har sau shida a cikin dare a Asmara babban birnin kasar.
A halin da ake ciki, asibitoci a Mekelle na fuskantar karancin magungunan jinyar wadanda suka jikkata, a cewar wasu jami'an agaji.