Kwararrun sojojin ruwan kasar Indonesia sun ce sun gano daya daga cikin bakaken akwatinan nadar bayanan jirgi daga tarkacen jirgin saman Lion Air mai lamba JT-610, wanda ya fada cikin tekun Java ‘yan mintoci kadan bayan tashinsa daga Jakarta a safiyar ranar Litinin.
Masu linkayar sun fadawa manema labaran tashoshin talabijin na kasar yau Alhamis cewa sun gano daya daga cikin na’urar nadar bayanan jirgin a can kasan teku sun kuma fito da ita.
Ma’aikatan ceto na ta aiki ba dare-ba-rana don gano tarkacen jirgin samfurin 737 Max 8, sun kuma gano na’urorin nadar bayanan jirgin, dake dauke da muhimman bayanai akan takaitaciyyar tafiyar da jirgin yayi, ciki harda magangannun karshe da matukin jirgin yayi da masu sa ido akan jirage dake kasa, a lokacin da ya nemi ya koma tashar jirgen saman.
Hukumomi sun fada jiya Laraba cewa, suna kyautata zato sun iya gano daidai inda jirgin saman na Lion Air yake a cikin teku, wanda ya bace daga na’urar bayanan wurin da jirgi yake bayan tashinsa zuwa tsibirin Bangka-Belitung dake kusa da Jakarta.