Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta ce Tana Da Hujjoji Akan Kisan Khashoggi


Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan

Kasar Turkiyya ta bukaci kasar Saudi Arabiya da ta bayyana ida suka kai gawar Jamal Khashoggi, sannan tana neman wani dan kasarta da aka yi amfani da shi wajan boye gawar.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayipp Erdogan ya bukaci hukumomin Kasar Saudi Arabiya a yau Jumma’a da su bayyana inda suka kai gawar dan jaridar nan na Amurka Jamal Khasoggi da aka kashe.

Hukumomin kasar har ila yau suna neman wani mutum da aka ce “na cikin gida ne” da aka yi amfani da shi wajen batar da gangar jikin dan jaridar, bayan da aka kashe shi a karamin ofishin jakadancin saudiya da ke Istanbul.

A lokacin da yake jawabi a gaban 'yan jam’iyyarsa ta AK Party a zauran majalisar dokoki, Shugaba Erdogan ya ce gwamnatinsa tana da karin hujjoji akan yadda aka kashe dan jaridar, amma kuma bai ba da bayanai dalla-dalla ba.

Sannan ya ce babban mai gabatar da kara na Saudi Arabiya zai ziyarci Istanbul ranar Lahadi inda zai hadu da jami’an kasar Turkiyyah a ci gaba da binciken da ake game da mutuwar Khashoggi.

A jiya Saudi Arabiya ta amince da cewa kisan Jamal Khashoggi shirya shi aka yi akan wasu bayanai da Turkiyya ta bayar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG