Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar samun gagarumar nasara a yayin wani aikin kakkabar da dakarun kasar suka gudanar a wasu sassan jihar Tilabery iyaka da Burkina Faso inda ‘yan ta’adda suka tilasta wa jama’a ficewa daga garuruwansu a farkon watan da muke ciki.
NIAMEY, NIGER - Tun a ranar 16 ga watan nan na Mayu ne sojojin Nijar suka kaddamar da ayyukan kakkaba a Yammacin kasar bayan da shugaba Mohamed Bazoum ya ba da umurnin gaggauta daukan matakan daidaita al’amura a Yammacin gundumar Torodi da Kudancin Gotheye na jihar Tilabery musamman garuruwan Bolsi ta 1 da Bolsi ta 2 da Banizoumbou inda jama’a suka arce sakamakon aika-aikar ‘yan ta’adda.
Sanarwar ma’aikatar tsaron kasa ta ce mako guda bayan soma wannan aiki dakarun tsaro sun halaka ‘yan bindiga 65 yayin da suka kona babura 163 sannan sun lalata ma’ajiyar kaya 12 da matattarar ‘yan ta’adda 11. Wannan al’amari ya dadada ran ‘yan Nijar.
A cewar mahukunta sojojin Nijar na ci gaba da matsa kaimi a yanzu haka a yankin Tilabery iyaka da Burkina Faso domin bai wa wadannan dubban mutane damar komawa garuruwansu ba tare da bata lokaci ba, matakin da wani jigo a kungiyar Sauvons le Niger Salissou Amadou ya yaba da shi kuma a cewarsa bai ma dace ba wannan yaki da ‘yan ta’addan yankin Sahel ya dauki lokaci mai tsawo.
A karshen makon da ya gabata ne kasar Nijar ta fara aiki da wasu sabbin jiragen saman yaki maras matuka kimanin 6 samfarin Bayraktar TB2 wadanda hukumomin kasar suka yi oda daga kasar Turkiya a ci gaba da karfafa matakan yaki da ta’addanci.
Masana sun bayyana wadannan jirage a matsayin masu jimirin wahala saboda yadda suke iya shafe awowi 24 cur suna shawagi a sararin samaniya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Souley Moumouni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5