Sojojin Najeriya Ya Kamata Ku Sani Ba'a Sauyawa Tuwo Suna

Masana harkokin tsaro da kare hakkin bil'adama, sun bayyana cewar kalaman babban hafsan sojojin na Najeriya basu dace ba, domin ba’a
sauyawa tuwo suna, kuma matakin bashi ne zai taimaka wajen yaki da
kungiyar ta Boko Haram a yankin Arewacin kasar ba.

Masana harkokin kare hakkin bil’adama irin su Kwamrade Musa Jika na
kungiyar Amnesty International, na cewa "wannan shiga hurumi ne
na 'yan jarida, domin kuwa 'yan jaridu ba karkashin hafsan sojoji Tukur
Burutai suke ba, don haka babu dalilin basu wannan umarni, kuma wannan alamu ne na cewar rundunar sojojin Najeriya sun gaza wajen yaki da 'yan Boko Haram, suna neman fakewa da 'yan jarida."

A bangare daya kuwa, shima wani tsohon hafsan sojojin saman Najeriya Iya
Kwamando Tijjani Baba Gamawa, yace wannan umarni ba za’a ce
ya dace ko akasin haka ba, domin duk duniya 'yan jaridu suna da
hurumin da suke aiki, kuma idan dai za’a tsaya ayi aiki bisa gaskiya, da
rikon amana, wannan ba wani abu bane na damuwa tsakanin sojojin da 'yan jarida.

Masu fafutukar kare hakkin bil’adama sun gargadi sojojin, dasu maida hankali wajen ayyukan sun, na tabbatar da tsaro a kasa ba tare da cin zarafin 'yan jaridu ko fararen hula ba.

Ga rahoton da wakilin muryar Amurka Babangida Jibrin ya hada cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Ya Kamata Ku Sani Ba'a Sauyawa Tuwo Suna