Sojojin Najeriya Sun Yi Ikrarin Gano Wata Makarkashiya Kan Zabe

Yayin da Najeriya ke fuskantar zabe a ranar Asabar mai zuwa, rundunar soji ta shida da ke Fatakol a jihar Rivers, sun gano ana shirin yin amfani da wasu bata gari domin ta da hankalin masu jefa kuri'a ranar zabe.

Rundunar sojojin Najeriya shiyya ta shida da ke birnin Fatakol a jihar Rivers ta ce, ta samu wasu bayanan sirri da suka tabbatar mata cewa wasu ‘yan siyasa sun debo wasu 'yan bangar siyasa daga jihohi daban-daban na yankin Naija Dalta da nufin haifar da tashin hankali a ranar zabe.

A wata sanar da mai magana da yawun rundunar sojoji ta shida, Kanal Aminu Iliyasu, ya rabawa manema labarai jiya, ta ce an gano an bai wa 'yan bangar siyasa makamai da kayan sawa na soja da za su ringa bi rumfunan zabe domin ta da hankalin masu zabe.

Rundunar ta shida ta ce, a shirye ta ke wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a a ko da yaushe kuma ako wane irin yanayi.

Yayin zabuka na siyasa a yankin Naija Dalta rayukan jama’a na salwanta a ko da yaushe kamar yadda tarihi ya nuna.

Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar Sokoto daga Fatakol:

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Yi Ikrarin Gano Wata Makarkashiya Kan Zabe