Sojojin Najeriya Sun Sake Yi Wa Kwamandojin ISWAP Rubdugu

Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce dakarun kasar sun hallaka wasu manyan
kwamandojin kungiyar ‘yan ta'addan ISWAP a yankin Alinwa dake arewacin
jihar Borno, a zirin yankin tafkin Chadi.

Mukaddashin daraktan sashen aikace-aikace na shelkwatar tsaron Najeriya ya bayyana cewa an cimma wannan gagarumar nasarar ne biyo bayan wasu bayanan sirri da rundunar ta samu akan wurin da manyan kwamandoji da mayakan na ISWAP ke taro don kitsa kai hare-hare a wasu sassan jihar Borno.

Hakan ya sa rundunar Operation Lafiya Dole ta tura jiragen saman yakinta wurin toron mayakan inda suka hallaka dukkan ‘yan ta'addan tare da kone wurin kurmus, harin da suka yi wa taken "Operation Decisive Edge," a cewar Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojan saman Najeriya Air Marshal Sadique Abubakar.

Tuni dai babban Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Najeriya Janaral Abayomi Gabriel Olonisakin ya jinjina wa dakarun tare da tabbatar da cewa sojojin kasar zasu ci gaba da daukar matakan soji har sai an kawo karshen ‘yan ta'addan

Masanin harkokin tsaro Dr. Kabiru Adamu, ya ce irin wannan kokarin da sojin kasar suke yi yana da tasiri sosai kuma idan aka ci gaba da yin haka ba tare da kakkautawa ba, tabbas za a kawo karshen 'yan ta'addan.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Sake Yi Wa Kwamandojin ISWAP Rubdugu