Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram Fiye Da 100

Sojojin Najeriya akan wata motar yaki a lokacin da suke zagaye a wata karamar kasuwa a birnin Maiduguri.

Rotanni da ke fitowa daga jihar Borno na nuna da cewa rundunar sojan Najeriya sun sami nasarar hallaka wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, har fiye da 100 a wani sumame da ta kai kan wasu ‘kauyuka.

Rundunar Sojan Najeriya dai sun farma maharan ne lokacin da suke cin kasuwar ‘kauyen Boboshe dake karamar hukumar Dikko a jihar Borno. Inda aka ce ‘yan Boko Haram sun mayar da wannan kasuwar tamkar tasu, wanda sukan ci kasuwar duk mako.

Ankai hari kan wasu kauyuka biyu inda rundunar tace ta kashe ‘yan kungiyar da dama, wanda suka hada da kauyen Mamuwari da Garidawaji dukkan su a karamar hukumar Dikko a Jihar Borno.

Mataimakin gwamnan jihar Borno Alhaji Usman Mammam Durkwa, ya ziyarci garin na Dikko, bayan fafatawa da rundunar sojan Najeriya tayi da maharani, kuma domin ya ganewa idonsa halin ‘yan gudun hijira ke ciki.

Sai dai ‘yan gudun hijirar da suka fito daga kananan hukumomin Mafa da Marte Dangala da Bama da Gwoza da kuma Kala Balge, ance adadinsu ya kai sama da dubu hamsin. Suna kuka ne kan karancin abinci da ruwan sha.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Najeriya Sun Kashe Mayakan Boko Haram Fiye Da 100 - 3'57"