Kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi dai na daga cikin masu fama da hare haren 'yan bindiga na bangaren Buharin Yadi.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce rundunar sojan Najeriya ce ta yi nasarar hallaka ‘dan bindigar da tawagarsa a dajin da ke kananan hukumomin Giwa a jihar Kaduna da kuma Sabuwa a jihar Katsina, kamar yadda mukaddashin kwamishinan tsaro na jihar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya tabbarwa Muryar Amurka.
Dama dai masana harkokin tsaro sun sha ba da shawarar a bi 'yan bindiga har mafakarsu maimakon jira sai sun kai hari, a saboda haka masani kan harkokin tsaro Manjo Janar Yahaya Shinko mai ritaya ya ce kokarin da sojojin suka yi abin a yaba ne, amma akwai sauran jan aiki a gaba saboda har yanzu akwai bukatar jami'an tsaro su yi aiki na bai-daya a jihohin da 'yan bindigar ke addaba.
Manoma a karamar hukumar Giwa irinsu malam Adamu Imani, na ganin nasarar hallaka 'yan bindiga ka iya zaburar da manoma su koma gona yin ayyukansu a yankin.
Hare-haren 'yan bindiga a wasu yankuna na jihar Kaduna dai sun takaita noma a bara, sai dai kuma ana ganin idan jami'an tsaro su ka ci gaba da maida hankali kan magance matsalar hare haren 'yan bindigar, akwai yuwuwar manoma zasu koma gona a bana.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5