Sojojin Najeriya Na Tsare Da Shugaban 'Yan Shi'a

Sojojin Najeriya sunce suna tsare da shugaban ‘yan Shi’a na Najeriya, bayan zargin da akayi cewa kungiyar ta kai hari kan ayarin motocin hafsan hafsoshin sojojin Najeriya.

Da yake magana da manema labarai a jiya litinin Major Janal Adeniyi Oyebade yace, yanzu haka suna tsare da Ibraheem Zakzaky da matarsa bayan da suka kai hare hare har wurare uku. Oyebade yace an kama Zakzaky a garin Zariya dake jihar Kaduna. Ya kuma ce an samu asarar rayuka a bangarorin biyu alokacin da aka kai hare haren na ranar Asabar da Lahadi, amma bai fadi yawan mutanen da suka mutu ba.

Kungiyar ‘yan Shi’a ta Najeriya tace sojoji sun kashe mata mutane har 300 a Zariya. Wasu rahotannin kuwa na cewa 20 ne kadai aka kashe.

Baki daya bangarorin biyu sun tabbatar da harin da aka kai gidan Zakzaky dake Zariya. Kamfanin dillancin labaru na Associated Press ya fitar da rahoton da ke cewa biyu daga cikin wuraren da aka kai ma hare-hare, wuraren ibada ne.

Kamar yadda wasu shedu sukace, tashin hanlin dai ya fara ne ranar Asabar, bayan da ‘yan kungiyar Shi’a suka rufe wata babbar hanya, suka kuma fara jifan ayarin motocin hafsan hafsoshin soja Janal Tukur Buratai. Wani mai magana da yawun rundunar sojan Najeriya ya kira jifar a matsayin yunkurin kashe shugaban soja.

Kungiyar Shi’a dai tace babu wani yunkurin kashe shugaban, kuma sojojin dai sun kaiwa kungiyar shiryeyyen hari ne kawai.