Tun farko dai da sanyin safiyar ranar Asabar gomman mayakan na Boko haram suka tattaru a wani sansaninsu, dake dajin na sambisa a bangaren yankin Gaizuwa ta bangaren yankin karamar hukumar Bama, inda bayanai ke tabbatar da yiwa yan ta'addan mummunar barna.
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatarwa muryar Amurka kai wannan farmaki, amma ba ta yi wani karin bayani ba ya zuwa lokacin rubata wannan labari ba a kamala wannan aiki ba, amma wasu jami'an sojin dake taka rawa wajen kai farmakin sun shaidawa muryar Amurka cewa wannan farmaki na daya daga cikin muhimman nasara da aka samu cikin wannan shekara ta 2023.
Yan ta'addar kungiyar Boko Haram wadanda ke fama da rikicin cikin gida a tsakaninsu, sun taru ne a wuri guda lokacin da jiragen yaki samfurin SUPER TUCANO suka afka masu, wajen harba boma bomai da rokoki al'amarin da bayanan farko ke nuna cewa lalle an yi musu kazamin barna.
Farmakin ya yi sanadiyyar halaka da dama daga cikin yan ta'addan da kuma kubutar da wasu fararen hula, kana wasu mayakan da suma suka tsira daga bisani sun mika wuya ga Brigade na 21 na rundunar OPERATION HADIN KAI dake yaki da yan ta'addan
A halin yanzu, sojojin kasa sun kutsa yankin inda kuma nan gaba kadanne za sami cikakken karin bayani dangane da hakikanin barnar da jiragen yakin sukaiwa yan ta'addan.