, Rundunar hadin guiwar ta kai farmakin na baya bayannan a yankunan Tumbin rago, Tumbin dilla da Jamina inda suka yi wa yan ta'ddan diran mikiya.
A wata sanarwa da kakakin rundunar dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Chadin Laftanar Kanar Kamaruddin Ademola Adegoke, yace farmakin da aka kai tare da tallafin jiragen yaki na rundunar ta MNJTF da kuma jiragen yakin sojin saman Najeriya nan take dai an kashe manya manyan mayakan Boko haram da ISWAP guda ashirin da biyar.
Bugu da kari Kanar Adegoke yace an kuma kwato dimbin makamai ciki har da wata babbar bindigar harbo jiragen sama, motar yaki da daruruwan harsasai masu rai, da wata motar da aka girke mata bindiga, babura goma sha daya da wani karamin yaro dan shekara biyar mai suna Bahna da mayakan suka gudu suka barshi a sansanin.
Dakarun sun dai kone sansanin kurmus sannan a wani farmakin na sojojin yankin tafkin Chadin suka kai a yankin Wulgo ta gefen Kamaru ta kasa da kuma ta ruwa nanma sun hallaka wasu mayakan Boko Haram biyar tare da kwato dimbin makamai iri iri.
Duka dai wadannan farmaki ana kaisu ne karkashin farmakin nan mai take OPERATION LAKE SANITY da babban kwamandan sojojin tafkin Chadin Manjo Janaral AK Ibrahim yace yanzu sun daina jiran 'yan ta'addan sai sun kawo hari sannan a kare kai, amma za yi ta binsu ne har inda suke.
Kwararru kan yankin tafkin Chadin irinsu Dr. Abubakar MS dake cewa lalle wannan sabon salo zai kai ga cimma samar da zaman lafiya ya nemi jama'ar dake zagayen tafkin su hada kai da dakarun don kwalliya ta biya kudin sabulu.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5