Sojojin Kasar Myanmar Sun Kai Samame Wata Kafar Yada Labarai

Myanmar

Yayin da sojojin Myanmar suke ci gaba da yaki da 'yancin fadi sonka, sojojin kasar ta Myanmar, sun bayyana kama wani tsohon ministan yada labarai a kasar.

Sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Myanmar sun kai samame wata kafar yada labarai ta Rakhine tare da kama wani dan jarida da ma’aikacin ofishin, kamar yadda Sashen Burma Na Muryar Amurka ya rawaito, lamarin da ya kara jaddada yadda sojoji ke murkushe kafafen yada labarai a fadin kasar bayan juyin mulkin da su ka yi.

An dai kai samame a ofishin Kungiyar Raya Kafafan yada Labarai na DMG da yammacin ranar Lahadin da ta gabata. Zaw Zaw, shi ne mai magana da yawun kafar yada labaran; ya shaida wa Sashen Burma Na Muryar Amurka cewa, sun kwace kayan aiki tare da kama wani dan jarida da wani mai gadi.

A wannan ranar, sojojin na Myanmar sun sanar da kama wani tsohon jami’in soja wanda ya taba rike mukamin ministan yada labarai a karkashin gwamnatin da ta gabata mai samun goyon bayan soji.