Dakarun na kasar Kamaru da ake kira da suna ‘Operatin Alfa’ sun kutsa ne cikin Najeriya don farautar ‘yan Boko Haram, kan hanyar su ne sukayi rashin sa’ar hawa kan wata nakiya da aka binne akan hanya, wadda tayi sanadiyar raunata sojojin Kamaru biyu.
Rundunar sojojin sun shiga garin Ngoshe mai tasarar kilomita 22 daga garin Ashigashiya, inda sukayi artabu har suka halaka mayakan Boko Haram da dama, aka kuma kama wasu maharan da suka ajiye bindigoginsu suka mika ‘kafa.
Dakarun an Operatin Alfa dai sun gudanar da wannan kutse ne domin samun damar bude hanyar Bama da Banki zuwa Marwa inda ‘yan kungiyar Boko Haram ke cin karensu babu babbaka.
Mai bada shawara kan harkar tsaro a Kamaru, Maigana Abba, yace sojojin Kamaru sun shiga Najeriya ne da sunan dakarun yankin tafkin Chadi, domin bude hanyoyin da aka rufe a dalilin ‘yan Boko Haram. Ya kuma cewa an sami nasara a wannan aiki da sojojin suka yi.
Domin karin bayani saurari rahotan Awwal Garba daga Kamaru.
Your browser doesn’t support HTML5