Kasar Kamaru ta bayyana cewa sojojinta tare da na Najeriya sun ceto daruruwan mutane da ‘yan boko haram suka yi garkuwa dasu, sannan sun kashe fiye da ‘yan ta’addar na Boko Haram kusan 100 a wani samamen da suka kai.
Kwamandojin askarawan sun ce, hakan ta faru ne lokacin da suka yiwa wani gari mai suna Kumahe dirar mikiya akan iyakar Najeriya da Kamaru, a wani shirin ratattakar ‘yan Boko Haram din da suka yiwa garin katutu.
Harin sojin ya share kwanaki 3 ana yinsa kafin samuwar wannan nasarar ta cetar jama’a. ba dai wata hujjar da ta tabbatar da wannan rahoton, abinda ya biyo bayan rahoton jiya na tattaunawar Sojin Amurka da Najeriya don kai mashawartan soji zuwa Maidugurin Najeriya.
Wani jigo a Amurka ya fadawa Muryar Amurka cewa ana nan ana tattauna yiwuwar kai mashawartan sojojin zuwa jihar Borno don bada shawarwarin yakar ‘yan Boko Haram, sai dai yace har yanzu baa kai ga matsaya ba tukunna.