Sojojin Iraqi da Na Amurka Basu San Inda Shugaban ISIS Yake Ba

Dakarun Iraqi suna dadakutsawa Mosul a yakinsu da kungiyar ISIS.

Tun makkoni da dama sojojin Iraq da na Amurka ke baiwa rufa baya suna ta matsawa zuwa kusa da garin Mosul wanda suke kokarin su kwato daga hannun ISIS – sai dai kuma abu daya yake damunsu: basu san inda shi madugun ISIS din, Abu Bakr Baghdadi yake ba.

Kakakin rundunar sojan na Amurka Col. John Dorrian ya tabattarwa manema labarai dake Pentagon cewa basa da masaniyar inda Baghdadi ya shiga, har ya kara da cewa, “inda mun san inda yake, da tuni yana Lahira.”

Da yake ba tabbas na inda yake, yanzu ana ta baza jita-jita dangane da hakan.

Su dai jami’an gwamantin Iraq sun nace akan cewa al-Baghdadi yana nan cikin Mosul, boye a cikin ramukkan karkashin kasa ko wasu lunguna, yana jan ragamar famar da dakarunsa ke yi na kare birnin.

Akwai kuma wasu kafofi da suka ce al-Baghdadi yana birnin Baghdaza, yana shirya wa mutuwa, har ma yana son tsaida wanda zai gaje shi a matsayin shugaban kungiyar ta ISIS.