Sojojin Hadin Gwiwa Sun Fatattaki Mayakan Boko Haram

Sojoji daga Nijar da Chadi da suka kwato garin Damasak dake Najeriya daga hannun mayakan Boko Haram sun gano gawarwakin mutane akalla Saba’in. Yawancinsu an yi masu yankan rago kana aka jefar dasu karkashin wata gada kamar yadda wani ganao ya shaida.

Rundunar hadin gwiwa ta kasashen yankin Takin Chadi tace ta fafata da mayakan Boko Haram, akan zirin da ya raba tsakanin Najerya da Nijar.

A cewar kakakin rundunar kanal Mohammed Dole, yayi wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina karin bayani. Inda yace sojojinsu sun sami nasarar shiga garuruwan dake kan iyakar Najeriya da Nijar, inda suka fatattaki mayakan Boko Haram daga kauyukan da suke boye a yankunan.

Da taimakon sojojin sama na Najeriya da Nijar da Chadi, yanzu haka dai sojojin Najeriya da ake kira Operation Lafiya Dole, sun sami shiga kauyukan sun zauna domin tabbatar da cewa ba a bar sauran mayakan Boko Haram a kauyukan ba.

Duba da yadda dakarun hadin gwawar suka fatattaki mayakan na Boko Haram, masana tsaro na fargabar zasu iya sulalewa cikin kasashen wannan yanki su kuma ci gaba da tafka aika aika. Amma hedikwatar tsaron Najeriya na tace a bangarenta babu wata fargaba, don mayakan Najeriya ta kan iyakoki suna cikin shirin ko ta kwana, a cewar daraktan watsa labarai na hedkwatar tsaron Janal Rabe Abubakar.

Saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Sojojin Hadin Gwiwa Sun Fatattaki Mayakan Boko Haram - 2'26"