A taron masu ruwa da tsaki na lamuran ayyukan Hajji, shugaban hukumar Barista Abudullahi Muktar Muhammad, yace Saudiyya tayi togaciya, inda tace zata iya dawo da wanda aka samu da saba wannan umarnin, wanda har ila yau ya hana ‘daura Guru ko Laya ko Daga.
Taron dai ya gudana karkashin jagorancin Sultan Mohammad Sa’ad Abubakar wanda Alhaji Yahaya Abubakar ya wakilta, ya sami halartar manyan malamai irin su Sheik Sa’idu Hassan Jingir wanda yayi kira ga yin guzurin tsoran Allah, inda yace duk wanda zai je hajji ana bukatar yayi guzurin abu biyu, na farko shine tsoron Allah, abu na biyu kuwa shine abin da mutum zai bukata ya ci.
Bara dai Alhazan Najeriya da dama na daga cikin Alhazan duniya da suka rasa ransu a hanyar zuwa jifan Shedan, wasu Alhazan Najeriya su Shida na daga cikin wadanda suka rugamu gidan gaskiya yayin fadowar kugiyar gini a babban Massallacin Ka’aba, wanda ya sanya Saudiyya dakatar da bayar da kwangila ga kamfanin nan na Bil Laden a lokacin.
Saurari cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.