Sojojin Amurka Uku Sun Mutu Bayan Tashin Wani Bam

An Kashe Sojojin Amurka Da Ba'Amurke Dan Kwantiraki A Wani Harin Bam Da Aka Kai, A Tsakiyar Gabashin Birnin Ghazni Dake Afghanistan.

Rundunar sojin Amurka da ke kasar Afghanistan ta ce an kashe mata dakaru uku, sannan an raunata wasu uku a lokacin da wani bam hadin-gida ya tashi a kusa da tsakiyar gabashin birnin Ghazni.

Daga cikin wadanda suka ji raunin, har da wani ba’Amurke dan kwantaraki.

Wata takaitacciyar sanarwa da aka fitar daga birnin Kabul, ta ce “an kwashe darakun Amurkan da dan kwantaraki da suka ji rauni, kuma suna samun kulawa a Asibiti.”

Sai dai sanarwar ba ta yi cikakken bayani kan wannan harin ba. Wannan kisan dakarun na Amurka a yau Talata, ya kawo jimillar sojojin Amurka da aka kashe a Afghanistan zuwa 11.