Gwamnatin kasar dai ta tura mukaddashin babban hafsan soji mai kula da runduna ta uku dake Jos,wato GOC, Birgediya Janar Benjamin Ahanotu da kwamandan rundunan soji ta 23 dake Yola Birgediya Janar Bello Muhammad da manyan jami’an tsaron jihar domin ceto da kuma debo gawarwakin dake sunkuru,wanda isa wurin sai da sojoji.
Da yake bayani babban hafsan soji mai kula da runduna ta uku dake Jos,wato GOC, Birgediya Janar Benjamin Ahanotu wanda ya jagoranci wannan tawagar gani da idon,ya yi tur da Allah wadai da irin rayukan da suka salwanta.
Yace,’’ Kai abun takaici ne abubuwan da muka gani ,na kisan da aka yi,tamkar dama akwai wani shiri ne na kisan kare dangi.An kashe kananan yara da mata masu ciki,sai kace Boko Haram. Ai ko Boko Haram wasu lokutan sukan bar kananan yara,haba. Wadanda suka tsira sune kawai wadanda suka gudu.
‘’Ai wannan kissan kiyashi ne ake son yi da wasu yan siyasa suka kitsa shi.
Shima da yake karin haske kwamishinan yan sandan jihar Taraban Yakubu Babas ya tabbatar da karuwan adadin wadanda aka kashen da kuma kokarin da ake yi a yanzu na maido da doka da oda.
To sai dai kuma gwamnan jihar Taraban Arch.Darius Dickson Isiyaku ya musanta zargin cewa yana da hannu da kuma sakaci game da wannan tashin hankalin.
Gwamnan dai cewa yayi, ‘’Ina mamaki da wasu ke zarginmu,ai ba yadda gwamnati zata bari a kashe mata jama’a,haba a fadi gaskiya mana. Ai mun samu rahoto tun farko kuma har mun kafa kwamitin bincike to amma tun kafin kwamitin ya soma aiki sai ga tashin hankalin ya auku,to me ake son mu yi?’’
Kawo yanzu dubban jama’a ne wannan rikici ya raba da gidaje a yankin Mambillan inda wasu suka ketara zuwa kasar Kamaru yayin da wasu kuma suka fantsama wasu kananan hukumomi dake makwabta da yankin.
Ga karin bayani daga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5