Biyo bayan tashin hankalin da ake samu a yankin Mambilla dake jihar Taraba, yan majalisar dattawa da kuma sauran shugabanin al’umma suna kira ga gwamnatin tarayya da ta hanzarta tura jami'an soja zuwa yankin.
Wannan sabon kiran dai ya biyo bayan sabbin rahotannin dake cewa duk da matakan da aka dauka tun farko, yanzu haka ana samun harin sari-ka-noke a wasu yankunan tsaunin Mambilan, kuma wannan na zuwa ne yayin da wadanda rikicin ya rutsa dasu ke cikin mawuyacin hali.
Senata Yusuf A.Yusuf dake wakiltar mazabar Taraba ta tsakiya a majalisar dattawa, ya mika kokon baransu ga gwamnatin tarayya da ta kai musu dauki na kara tura jami’an tsaro musamman sojoji tare kuma da tallafawa wadanda yanzu ke gudun hijira a ciki da kuma wajen Najeriya.
Shima da yake karin haske, dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar mazabar Nguroje Barr.Muhammad Bashir Bape ya musanta yadda wasu ke danganta tashin hankalin da fadan addini.
Rundunan yan sandan jihar Taraban ta tabbatar da harin sari-ka-noken da ake samu, to amma ta bada tabbacin kare rayuka da kuma dukiyar al’umman jihar inda tace za’a tura karin jami’an tsaro kamar yadda ASP David Misal kakakin rundunan yan sandan ke cewa.
Tsaunin Mambila dake iyaka da kasar Kamaru, yanki ne dake da albarkatun noma da kiwo kuma wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ke haramar soma aikin samar da wutan lantarki na madatsar Mambila daka iya baiwa jihohin arewa maso gabashin Nigeria wuta.
Ga abunda senata Yusuf A Yusuf mai wakiltar Taraba ta tsakiya majalisar Dattijan Najeriya ya gayawa Ibrahim Abdulaziz.
Facebook Forum