WASHINGTON DC - Wata majiya daga rundunar sojin ta bayyana cewar an kubutar da mutanen ne yayin wani aikin sintiri a kauyen rimi bayan da suka shafe kwanaki 46 a hannun 'yan bindiga.
Wadanda da aka kubutar din na daga cikin mata 54 da aka sace akan hanyar Gamji zuwa Dandume a farkon watan Fabrairun daya gabata.
Biyo bayan kubutar dasu da aka yi a jiya litinin, an mika matan da yaran hannun Shugaban Karamar Hukumar Sabuwa, wanda shi kuma ya sadasu da danginsu.
Da yake tabbatar da afkuwar lamarin, Gwamna Dikko Radda cikin wata sanarwa da babban sakatarensa akan harkokin yada labarai Ibrahim Kaula Muhammad ya fitar a jiya Litinin, ya yabawa dakarun saboda jarumta da daukar matakin daya dace da suka yi.
Gwamnan wanda ya jinjina girman lamarin, ya baiwa al'umma tabbacin kudirin gwamnatinsa na kawo karshen matsalar 'yan bindiga a fadin jihar Katsina.
A cewar sanarwar, aikin kubutar da wadannan mata da yara shaida ce game da kwarin zuciya da jajircewar dakarun tsaronmu. Mun kudirin aniyar sama musu dukkanin kayan aikin da goyon bayan da suke bukata domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al'umma.