Wani dan jarida a babban birnin jahar ta Amhara ya fadawa wa Bashir Dar na Sashin Kuryar Afirka na Muryar Amurka cewa An kashe Janar Asamnew Tsige ne a jiya Litinin, yayin da ya ke kokarin tserewa jami’an tsaro.
A halin yanzu kuma, wani jami’i da ya ji rauni a lokacin da aka yi yunkurin juyin mulkin na ranar Asabar, wanda shi ne mai gabatar da kara na yankin Migbaru Kebede, ya mutu sakamakon raunukan da ya samu, a cewar wani rahoto da kafar yada labaran gwamnatin kasar ta bayar.
A ranar Asabar ne wasu yan bindiga suka kutsa kai cikin wani taron da ake yi a Bashir Dar, inda suka kashe shugaban yankin , Ambachew Mekonnen, da kuma daya daga cikin manyan masu bashi shawara.
Kafafen yada labaran gwamnati sun bayyana Janar Asamnew, wanda shi ne shugaban jami’an tsaron jihar Amhara, a matsayin wanda ya jagoranci yukurin juyin mulki.