Yayin da sauran duniya ke hidimar bikin sabuwar shekara, al'ummar Borno kuwa zasu kasance cikin kulle har na kwanaki biyu.
Rundunar sojojin Najeriya dake Maiduguri ita ta fitar da wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da mutane na rundunar Kanal Usman ya aikawa manema labaru. A sanarwar sun haramta zirga-zirgan ababen hawa a birnin Maiduguri da kewaye.
Kanal Usman yace sun haramta duk ababen hawa, motoci, babura, kekuna, da babura masu kafafuwa uku da ake kira keke napep, har ma da jakuna da dawakai. Sanarwar ita ce ta farko da sojojin suka dauki irin wannan matakin ba tare da bada wani dalili ba.
Sojojin sun nemi goyon bayan jama'a domin wai, sun dauki matakin ne domin kare rayukan jama'a da dukiyoyinsu.
Sai dai kuma tsagaita zirga-zirga a wannan lokacin ya fada lokacin da za'a gudanar da mauludi. Shugaban Zawiyar Madinatu Halifa Ali Abdulfatahi yace ranar mauludi zasu karanta dabi'o'in Annabi da tarihinsa da kuma yin addu'o'i musamman ga kasa ta samu zaman lafiya. Alherin da ake samu a mauludi ya fi hanashi da ake son a yi.
Saidai Sheikh Mutallab Abdullfatahi ya nuna rashin gamsuwarsa da matakin da sojojin suka dauka ba a wannan lokacin.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5