Shekara takanzo ta wuce, akan farayima sabuwar shekara shiri tun daga wantan Nuwamba, wadda akasarin mutane a duniya kanyi wasu alkawulla ko wasu fatan cinma wasu bururukansu a cikin sabuwar shekara. Ta bangaren gwamnatoci kuwa sukan yi shiri don gabatar da kasafin kudin sabuwar shekara da ma yadda za’a kashe kudaden.
A wannan shekar mun samu zantawa da wasu ‘yan Najeriya mazauna kasashe daban daban da sukayi muna bayani dangane da yadda ake gudanar da bukukuwan sabuwar shekara a kasashen da suke. A tabakin Sarkin Hausawa a birnin Wagadugu ta kasa Barkinafaso, yace a dai kasar ta barkinafaso biyowar bayan chanza shugaban kasar da akayi bada dadewaba, yasa kasar tana cikin kwanciyar hankali al’umar kasar na cikin farinciki. Akwai zaman lafia a tare da jama’a, amma dai babban abun damuwa shine babu kudi a tare da jama, talauchi yayi katutu.
Amma abun da ake sa rai shine idan sabuwar gwamnati ta zauna da kafafunta to ba’a cire tsammanin komai zaiyi dai daiba. Shi kuma Mal. Usman Isyaku me karatun likitanci a kasar Ingila, yace mutane dai nata hada hada kaiwa da kawowa don shiryama sabuwar shekarar wanda kusan kudin wasu abubuwa na sauka wasu kuma na kara hawa saboda shirin sabuwa shekarar. Kuma ya kara da cewar abu mafidamuwa a kasar shine yadda kasar ke kokarin ganin ta magance matsalar bakin haure da suke kawoma kasar matsalar tattalin arziki, wadannan dai bakin hauren na zuwa daga kasashen gabashin turai ne.
Ta bakin Dr. Lukman Salihu, wanda ke zaune a kasar Saudiya, yace kasar dai kasancewar ta kasar Musulunci, basu da wani abu da sukeyi wanda yashafi sabuwar shekarar turawa, illa dai sukan gabatar da kasafin kudinsu na sabuwar shekara. Babban abu da kawai za a ga banbanci shine yadda ake biyan ma’aikata yan kasar waje albashi da tsari irin na turawa, baya gashi babu wani abu da akeyi na bukin shekara a kasar Saudi Arebiya.
Babban abu me daukan hankali a kasar Najeriya, a wannan bukin na sabuwar shekara shine maganar zaben dake karatowa, al’uma dai na meda hankalinsu ne akan yadda zaben kasar zai kasance. Kana kuma akwai maganar rashin tsaro a kasar.