Sojoji Sun Damke Wani Rikakken Dan Ta’adda Tare Da Kubutar Da Mutanen Da Yake Garkuwa Dasu A Filato

Sojojin Najeriya a wani aikin sintiri da suka yi (Facebook/ Nigerian Army)

A sakon da ta wallafa a shafinta na X a yau Juma’a, rundunar sojin na cigaba da kai zafafan hare-hare akan ‘yan ta’adda a ko’ina a fadin Najeriya.

Rundunar Sojin Najeriya ta bayyana cewar dakarunta sun kama wani rikakken dan ta’adda da aka jima ana nema, Hussein Usman, a kauyen Ganawuri, dake karamar hukumar Riyom ta jihar Filato tare da kubutar da mutanen da yake garkuwa dasu.

Rundunar ta kara da cewa dakarunta sun kuma kwace makamai da sauran muhimman kayayyakin da ‘yan ta’addar ke amfani dasu, inda ta kara tsaurara matakan da take dauka akan batagarin dake boye a cikin dazuzzuka.

A cewar rundunar, bayan samun sahihan bayanan sirri a ranar 11 ga watan Satumbar da muke ciki, dakarunta dake jihar Filato sun yi nasarar kama dan ta’addar da aka jima ana nema, Usman Hussein, wanda ya bayyana cewa shine yake kitsa munanan hare-haren da ake kaiwa a jihar Filato.

A yau ne rahotanni daga jihar Zamfara suka tabbatar da nasarar hallaka kasurgumin dan bindiga nan Halilu Sububu.