Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Goyi Bayan Afirka Wajen Neman Kujerun Dindindin A Kwamitin Sulhu Na Majalisar Dinkin Duniya


United Nations Assembly
United Nations Assembly

Thomas- Greenfield ta shaida wa Kwamitin Hulda da kasashen Wajen cewa “Shekara da shekaru, kasashen nahiyar suna ta kiraye-kiraye a samar da wata majalisa mai kunshe da wakilai, wacce za ta nuna kowane yanki na duniya

Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta sanar a ranar Alhamis cewa, Amurka na goyon bayan samar da kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Sulhu na Majalisar ga kasashen Afirka da kuma kujera guda daya da za’a yi karba-karba a tsakanin kananan kasashe masu tasowa da ke kan Tsibirai.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Amurka ke kokarin gyara alaka da kasashen Afirka, inda da dama ba su ji dadin yadda Washington ke goyon bayan yakin da Isira’ila ke yi a Gaza ba, da kuma zurfafa dangantaka da kasashen tsibirin Pacific wanda ke da muhimmanci ga dakile tasirin China a yankin.

Thomas- Greenfield ta shaida wa Kwamitin Hulda da kasashen Wajen cewa “Shekara da shekaru, kasashen nahiyar suna ta kiraye-kiraye a samar da wata majalisa mai kunshe da wakilai, wacce za ta nuna kowane yanki na duniya a yau sannan ta mai da hankali akan kalubalen da muke fuskanta a yau.”

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG