Sojoji Masar Sun Kai Farmaki Kan Masu Zanga Zanga

Wani dan zanga zaga yake nuna hnau jina jina,bayan da jami'an tsaro suka kai farmaki kan dandalin Tahrir,da nufin tarwatsa masu zanga zanga.

‘Yan zanga zanga a Masar sun sake hallara a dandalin ‘yanci ko Tahrir,bayan wani mummunar farmaki da aka kai kan masu zanga zangar da suka kwana suna zanga zangar nuna kin jinin tsohuwar gwamnati da ma sabbin shugabannin kasar.

‘Yan zanga zanga a Masar sun sake hallara a dandalin ‘yanci ko Tahrir,bayan wani mummunar farmaki da aka kai kan masu zanga zangar da suka kwana suna zanga zangar nuna kin jinin tsohuwar gwamnati da ma sabbin shugabannin kasar.

Da misalin karfe uku ne asubahi ne ‘Yansanda soja suka fantsama cikin dandali da kula kai da harba bindigogi,domin tarwatsa masu zanga zangar d a suka biris da dokar hana yaweomn dare.Wasu majiyouin kiwon lafiya sun ce an kashe mutane biyu wasu da dama kuma suka jikkata.

Shaidu suka ce an doki masu zanga zanga,har ma an ga jinni kan tituna a safiyar yau Asabar.

Majalisar mulkin sojan kasar ta bada sanarwar cewa ‘Yansanda suna tunkarar masu zanga zanga a kokarinsu na ganin an mutunta dokar hana fita.Suna aza laifin tashin hankalin kan masu zanga zanga.

Masarawa suna kara nuna bacin ransu da shugabannin mulkin sojan kasar. Jiya jumma’a masu zanga zanga sun nemi a da cire shugaban kasar,Field Marshal Mohammed Hussein Tantawi.

Masu zanga zanga suka da’ira domin kare hafsoshin soja da suka shiga jerin masu zanga zangar,duk da umarnin rundunar sojin kasar da haramata musu yin haka.Zanga zangar ita ce mafi girma a babban birnin kasar tun da aka tilastawa tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ranar 11 ga watan Febwairu.