Rahotanni daga yankin Tilabery na cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari a yammacin jiya litinin, a barikin sojan kauyen Inates dake kan iyakar kasar Nijar da Mali, inda suka yi nasarar hallaka sojoji da dama kafin suka tsere.
Hukumomin kasar Nijar sun tabbatar da faruwar wannan hari da ke kara farfado da mahawara, akan dokar ta bacin da aka kafawa wasu 'yankunan kasar ne.
Da wajen karfe biyu da rabi na rana wasu motoci biyu dauke da boma bomai, suka kutsa barikin sojan kauyen Inates inda suka tarwatsa wajen, dai-dai wannan lokaci wasu mutane da ke kan babura suka bude wa barikin sojan wuta, inji wata sanarwar rundunar mayakan Nijar wacce aka rarrabawa kafafen yada labarai.
Sanarwar ta kara da cewa an shafe lokaci mai tsawo ana karawa tsakanin wadanan ‘yan bindiga da sojojin gwamnati, inda da ya haddasa asarar rayukan sojoji kimamin 18, inda wasu 4 suka yi batan dabo. Jami'an tsaron jamhuriyar Nijar sun kashe ‘yan ta’adda da dama, koda yake ba a bayyana adadinsu ba, sannan jiragen sojan sama sunyi luguden wuta akan wadanan maharan, sun kuma ragargaza wata babbar motar ‘yan ta’addan.
Sojojin Nijar da hadin gwiwar takwarorinsu na kasar Amurka sun bi sahun wadanan mahara da aka bayyana cewa sun doshi kasar Mali.
A watan Mayu da ya shige, ‘yan bindiga sun hallaka wa jamhuriyar Nijar sojoji kusan 30, akan iyakar kasar da Mali. A hirar da wakilin Muryar Amurka yayi da Ibrahim Mamoudou wani jami’in fafutikar kare hakkin dan adam, yace irin wannan al’amarin mai matukar tayarda hankali ne.
A yau Talata ne za'a yiwa gawarwakin wadanan sojoji jana’iza a garin Tilabery, inda jama’ar gari suka hallara domin amsa kiran hukumomi akan wannan bukata, koda yake wata majiya na cewa a garin Intanes za a yiwa wadanan mamata makwanci.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5