Hafsan Hafsoshin Najeriya, Manjo Janar, Taoreed Lagbaja shine ya kaddamar da rundunar mai lakabin ‘’ Operation Hakorin Damisa IV’’ ya ja kunnen jami’an sojin da su gudanar da aikinsu ba sani - ba sabo, babu nuna bangaranci don maido da zaman lafiya a Jahar Filato.
Bayan kammala kaddamar da rundunar Hafsan Hafsoshin ya garzaya dakin taro a wata makarantar firamare a cikin garin Mangu, dake dankare da dubban mutane, musamman mata da yara dake gudun hijira, inda ya gana da masu ruwa da tsaki, suka kuma tattauna batun zaman lafiya.
Shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Alla a karamar hukumar Mangu, Yahaya Bello Shanono ya bada tabbacin hadin kai don samun zaman lafiya.
Shugaban kungiyar raya kabilar Mwaghavul, Mr Joseph Gwankat ya yi fatan Allah ya baiwa hafsan hafsoshin basirar kawo karshen matsalar.
Shugaban riko na karamar hukumar Mangu, Honarabul Markus Artu ya ce ya sadaukar da kansa ne don tabbatar da an sami zaman lafiya a yankin na Mangu.
Babban basaraken Kasar Mangu, Mishkaham Mwaghavul, da John Putmang Hirse ya ja hankalin al’umma ne kan su yi hakuri da juna.
Daga karshen ganawar, hafsan hafsoshin na Najeriya, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya shaida wa mahalarta taron cewa dakarun za su kasance a yankin don tabbatar da zaman lafiya, don haka ya bukaci a basu goyon baya.
Rikicin na yankin Mangu da ya fara da kisan mutum guda ya fadada, inda rayuka fiye da dari biyu suka salwanta, an kuma kone gidaje da wuraren ibada, yayin da gonaki da dabbobi ma suka hallaka, dubban mutane ke gudun hijira, wasu ma ba’a san inda suke ba.
Saurari rahoton a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5