Wani wanda ya sami lambar yabo ta Nobel a Najeriya ya kafa jam'iyar siyasa

Masu kada kuri'a a Najeriya a rumfar zabe.

Dan Najeriyan nan da ya sami lambar yabo ta nobel Wole Soyinka ya kaddamar da sabuwar jam’iyar siyasa da zumar yakar cin hanci da rashawa.

Dan Najeriyan nan da ya sami lambar yabo ta nobel Wole Soyinka, ya kaddamar da sabuwar jam’iyar siyasa da zumar yakar cin hanci da rashawa da kuma tsuma matasa masu kada kuri’a. Membobin jam’iyar Democratic Front for a People’s Federation, sun zabi Soyinka a matsayin shugaban jam’iyar a wani zaman kaddamarwa da aka yi ranar Asabar. Soyinka yace ba zai tsaya takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar cikin shekara ta dubu biyu da goma sha daya ba. Sai dai bisa ga cewarsa, jam’iyar zata yi amfani da ikon muhawara wajen shata sakamakon zaben. Farfesan da ya sami lambar yabo ta Nobel, yace an kafa jam’iyar a matsayin gwaji, da nufin ganin ko yana yiwuwa a iya fada a ji a Najeriya, ba tare da kashe miliyoyin dala ba. Soyinka ya sami lambar yabo ta Nobel a shekara ta dubu da dari tara da tamanin da shida, ya kuma kasance mutum na farko a nahiyar Afrika da ya sami lambar yabon.