Siyasar Gazawa Daga Jam'iyyun Siyasa Ta Kankama A Najeriya

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osibanjo.

Kakar siyasa ta kankama a Najeriya, inda ake yakin neman zabe da bayyanar da gazawar wata jam'iyya.

'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da amfani da batun Boko Haram wajen yakin neman zabe, ganin yadda matsalar taki ci taki cinyewa, al'amarin da kowacce jam'iyya ke cewa in an zabeta zata kawo karshen matsalasr.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa matsalar ta kasa da kasa ce, abun ma da yasa suke hadakar kasashen yankin tafkin chadi don yiwa tufkar hanci, ya bayyana hadakar da cewa lalle kwalliya na biyan kudin sabulu.

A nata bangaren 'yar takarar mataimakiyar shugaban kasa a jam'iyyar YPP, Hajiya Umma Abdullahi Getso, tambaya tayi cewa, shin su wanene ma 'yan Boko Haram din? Wake daukar nauyinsu? tana cewa a baya dakarun Najeriya sun fita kasashen duniya kuma sunyi rawar gani, tana mamakin abin da ya basu samun nasara a cikin kasarsu ba.

Alhaji Ganiyu da ke takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar ACPN ya jaddada cewa in har 'yan Najeriya suka zabesu, to za suyi kokari su samarwa Najeriya da isassun makaman da zata gama da 'yan ta'addan.

Bisa ga dukkan alasmu dai wannan batu na Boko Haram ya zama wani babban batun da 'yan siyasar kasar suka makale dashi, suna yakin neman zabe a fafatawar da za ayi badi idan Allah ya kaimu, suna zargin gwamnatin APC da cewar ta gaza, yayin da gwamnatin ke cewa tana samun nasara.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasar Gazawa Daga Jam'iyyun Siyasa Ta Kankama A Najeriya 2'20"