Siyasa Da Son Zuciya Ke Ruruta Tashin Hankali A Jihohi: Mshelia

Ibrahim Kadafir Mshelia

Mai neman tsayawa takarar gwamna a jihar Borno karkashin tutar jam’iyar Labo, Kyaftin Ibrahim Kadafi Mshelia ya bayyana takaicin ganin siyasa da son zuciya sun hana a shawo kan rikicin da ake fama da shi a wadansu sassan arewacin kasar.

Da yake tsokaci a hira da sashen Hausa biyo bayan hare haren da aka kai a wadansu kauyukan Karamar Hukumar Barikin Ladi a jihar Plato, da rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kashe mutane tamanin da tara, da suka hada da mata da kananan yara, Kyaftin Mshelia yace, rashin kamawa da kuma tuhumar wadanda ake kyautata zaton suna da hannu a irin wadannan tashe tashen hankalin ya sa zai zama da wuya a iya shawo kan matsalar.

Ibrahim Kadafi Mshelia wanda ya fito daga kudancin jihar Borno inda ake fama da tada kayar bayan kungiyar Boko Haram ya bayyana cewa, rashin gaskiya yasa masu tada kayar baya suke cin karensu ba babbaka a kasar, kasancewa, duk da yake rikicin Libya ya haifar da kwararar makamai a kasashen Nahiyar Afrika, sai dai lamarin Najeriya yayi muni. Ya kuma bayyana takaicin ganin duk da kawancen da Najeriya ta kulla da kasashen dake makwabtaka da ita a yunkurin shawo kan kungiyar Boko Haram, har yanzu ana fama da matsalolin tsaro a kasar.

Ya bayyana cewa, tilas ne a manta da banbance bancen addini da kabilanci da siyasa da duk wani abinda ke kawo koma baya idan ana so Najeriya taci gaba. Ya kuma yi kira ga ‘yan siyasa su kasance masu kishin kasa, da burin inganta rayuwar talakawan da suke wakilta domin ganin an sami zaman lafiya mai dorewa da kuma walwala.

Saurari hirarshi da Grace Alheri Abdu

Your browser doesn’t support HTML5

Ibrahim Kadafi Mshelia Kan tashin hankali a jihohi-4:45