Siyasa Bada Gaba Ba: Kano Koda Me Ka Zo An Fika

Bayan kammala zabukan gwamnoni da aka gudanar a fadin Najeriya, tuni aka fara fitar da sakamakon wasu jihohin da suka kammala karbar sakamakon zabe, amma a jihar Kano ba haka abin ya faru ba, domin kuwa mataimakin gwamnan jihar Kano, da mukarabansa ne suka tada hargitsi a karamar hukumar Nassarawa.

A jiya ne a karamar hukumar Nassarawa aka samu hargitsi a wajen tattara sakamakon zabe na gwamna inda mataimakin gwamnan jihar Kano Alh. Nasiru Yusuf Gawuna, ya je wajen tattara sakamo da kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sulen Garo, da shugaban kungiyar ciyamomi na jihar Kano domin tada hargitsi domin lalata akwatunan zabe.

Abbah Isa ya ce ana tsaka da karbar sakamako ne wannan al’amari ya faru inda ake tsaka da aiki, cike da matasa da jami’an 'yan jarida da hukomin tsaro domin tabbatar da sun kare yancin su.

Ya kara da cewa da zuwansu ne suka farma baturen zaben da ke karbar sakamakon na karamar hukumar Nassarawa, da yunkurin kwace takardun zabe, tare da lalata takardun zaben har da watsa barkonon tsohuwa.

Ita kuwa malama Zulaiha cewa ta yi ko da aka sanya barkonon tsohuwa an karbi sakamakon akwatuna 10 ana kan na goma sha daya ne aka lalata al’amarin, inda mataimakin gwamna da mukarrabansa bayan tada hargitsin ne suka shiga motocinsu suka kuma nufi kofar fita.

Amma tuni jami’an 'yan sanda suka yi musu tara-tara aka rufe kofa suka kuma izza keyarsu motar 'yan sanda, sannan suka nufi shelkwatar 'yan sanda ta jihar Kano dake Bompai, domin cike ka’idojin kare hakkin al’umma da suka gudanar da zabensu.

Sun kara da cewa mataimakin gwamnan dai ya taho da odilansa wanda yake take masa baya, domin gudanar da wannan katobarar, da shi da Murtala Sulen Garo domin kwace kuri’un al’umma.

Your browser doesn’t support HTML5

Siyasa Bada Gaba Ba: Kano Koda Me Ka Zo An Fika 5'10"