Za a girke sojojin gwamnatin Siriya akan iyakar Siriyar da Turkiyya, don su taimaka wajen fatattakar sojojin Turkiyya da ke shigowa don yakar Kurdawan Siriya, a cewar jami'an Kurdawa jiya Lahadi.
Wannan yarjajjeniya ta ba saban ba da aka cimma tsakanin Kurdawa da Siriya da kuma Rasha - wadda babbar kawar Siriya ce - na zuwa ne kwanaki hudu bayan da sojojin Turkiyya su ka abka ma Kurdawa a arewacin Siriya bayan kusan dukkannin sojojin Amurka sun janye.
Turkiyya na daukar dakarun Kurdawa na kungiyar rajin kare demokaradiyya a Syrian a matsayin 'yan ta’adda masu hada baki da 'yan awaren da ke Tukiyya.
Masu saka ido sun ce a cikin kwanaki hudu kacal da su ka gabata, an kashe fararen hula akalla 60 baya ga wasu dubbai da su ka tsere.