Kasar Siriya ta caccaki Isra’ila akan kwashe daruruwan masu aikin agajin sa-kai na kungiyar White Helmets, tana mai yin Allah wadai da shirin da ta kira “babban laifi”.
tsawon lokacin da aka kwashe ana rikicin Siriya, gwamnatin kasar ta zargi ma’aikatan agajin da yin aiki da ‘yan tawayen dake samun goyon bayan wasu kasashe. Haka kuma Siriya ta sha dora laifin fadan, wanda aka fara a shekarar 2012, akan gwamnatocin wasu kasashen ketare, ta kuma kira masu adawa da mulkin shugaba Bashar al-Assad a matsayin ‘yan ta’adda.
A shekarar 2013 aka kafa kungiyar da ake kira Syria civil defense ko White Helmets da turanci, a matsayin kungiyar agajin gaggawa ta wadanda suka jikkata sanadiyar hare-hare ta sama da kuma wasu hare-haren a lokacin arangamar da aka yi tsakanin dakarun dake goyon bayan shugaba Assad da kuma ‘yan tawayen dake kokarin murkushe gwamnatinsa.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka a cikin wata sanarwa, ta yi na'aam da ceto wadanda ta kira, "gwarzayen masu aikin sa kai da suka ceto dubannan rayuka".