"A birnin Aleppo, akwai yiwuwar mu ga mummunar matsalar jinkai wadda ba a taba gani ba a tsawon shekaru biyar da aka yi ana zubar da jini da aikin rashin imani a yakin na Siriya," a cewar Stephen O'Brien ga Kwamitin Sulhun MDD a yawabinsa na wata-wata kan wannan batu.
"Kamar yadda na ce a baya, ya kamata in yi duk abin da na ke iyawa in jaddada bukatar tsagaita wuta ta tsawon sa'o'i 48 tare da yaddar bangarorin biyu, saboda a samu sukunin kai kayan agaji a dukkan sassan Aleppo."
Tun watan jiya MDD ta ke ta kiraye-kirayen a rinka tsagaita wuta na tsawon sa'o'i 48 a fadan da ake yi a Aleppo, saboda a samar da kayan agaji ga marasa lafiya da kuma wadanda su ka samu raunuka.
O'Brien ya ce a shirye MDD ta ke ta tura motocin daukar kaya da 70 makare da kayan agaji zuwa gabashin Aleppo da zarar ta samu cikakken tabbacin tsaro.