Babban Sipeton 'yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya ba da umurnin gano duk inda almajiran El-Zakzaky su ke don hukunta su bisa dokar yaki da ta'addanci ta 2013.
Wannan umurni ya biyo bayan hukuncin babbar kotun tarayya da ta yanke hukuncin haramta motsin tafiyar Shi'a ta El-zakzaky wato "Islamic Movement In Nigeria" da jama'ar El-Zakzaky ke fassarawa da Harkar Musulunci.
Muhammad Adamu na magana ne a taro da manyan jami'an rundunar a shelkwatar 'yan sanda a Abuja, inda ya ce, duk wani aiki na zanga-zanga ko wata mu'ammalar kungiyar ta kowanne bangare haramtacce ne.
Tun a 2014 shekara daya gabanin tsare El-Zakzaky, ya hango za a haramta tafiyar ta sa ta Shia.
Da ya ke magana kan matakin, daya daga masu zanga-zangar a Abuja Sulaiman Jibrin Kafanchan, ya ce su na fatar a sako jagoran su El-Zakzaky.
Masana shari'a na nuna an samu wani sabon hukunci daga kotun daukaka kara da ya saba da na babbar kotu, cewa tafiyar El-Zakzaky za ta ci gaba da zama haramtacciya.
Yanzu dai lokaci ne zai nuna ko almajiran na El-Zakzaky za su iya dakatar da muzaharar ko kuwa za su daukaka kara.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:.
Your browser doesn’t support HTML5