Tawagar kwallon kafar Sifaniya ta lashe kofin kasashen nahiyar Turai bayan da ta ci takwararta na kasar Ingila da ci 2-1
Washington DC —
Sifaniya ne ta fara zura kwallo jim kadan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci inda Nico Lewis ya farke.
Cole Palmer da ya shigo bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ya zura wa Ingila ana minti 73 da taka leda.
Sai dai da sauran minti 4 a kammala wasan Mikel Oyarzabal kara zura ma Sifaniya kwallo.
Wannan shi ne karo na hudu da Sifaniya za ta lashe gasar bayan ta lashe a 1968, 2008, 2012 da 2024.
Wannan shi ne karo na biyu a jere da Ingila ta kai wasan karshe a Euro, bayan da Italiya ta doke ta a Euro 2020 a bugun fenariti a Wembley.