Sifaniya Ta Kai Wasan Karshe Na Euro 2024

Euro 2024 Soccer Spain France

Tawagar kwallon kafar Sifaniya ta kai wasan karshe a gasar cin kofin nahiyar Turai ta Euro 2024 bayan ta ci Faransa 2-1 a filin wasa na Allianza Arena a birnin Munich na Kasar Jamus.

Faransa ce ta fara zura kwallo ta hannun Randal Muani bayan minti tara da fara wasa daga bisani Sifaniya ta rama ta hannun Lamine Yamal ana minti 21 da taka leda.

Ana minti 25 da buga wasa Dani Olmo ya bugu kwallo sannan Youles Kounde, dan wasan bayan Faransa ya sa kafa ta shige raga bayan ta riga ta wuce mai tsaron raga.

Sifaniya za ta buga wasan karshe da duk wanda ya yi nasara a wasa na biyu na semifainal tsakanin Ingila da Netherlands wanda za a buga karfe 8 na dare agogon Najeriya da Nijar, gobe, Laraba, 10 ga Yuli a filin wasan Westfalenstadion a birnin Dortmund da

Yamal ya kafa tarihin zama matshin da ya ci kwallo a gasar mai shekara mafi kankanta da shekara 16 da kwana 362.