Siasia Ya Gayyaci Wasu 'Yan Wasa, Ya Kori Wasu

ទិដ្ឋភាព​ទូទៅ​នៃ​កម្មវិធី​ «បុណ្យភូមិ» ដែល​ត្រូវបាន​រៀបចំ​ឡើង​ដើម្បី​បញ្ជ្រាប​ការ​យល់ដឹង​អំពី​ទម្រង់​វប្បធម៌​បុរាណ​ដល់​យុវជន​កម្ពុជា​ ក្នុង​វត្ត​ទួល​ក្រសាំង ​ខេត្ត​កណ្តាល​ នៅ​ថ្ងៃទី​៧ ខែ​មេសា​ ឆ្នាំ​២០១៧។ (ហ៊ាន សុជាតា/ VOA)

Babban kochin tawagar matasa ‘yan kasa da shekaru 23, Samson Siasia, ya kira ‘yan wasa har takwas daga cikin 'yan wasan Flying Eagles da Manu Garba ya hada, domin buga wasan neman zama zakarun Afirka da za’a fara wata mai zuwa.

Cikin ‘yan wasan da aka kira harda ‘dan wasan Manchester City Kelechi Iheanacho, da kaftin Musa Mohammed da Taiwo Awoniyi Kingsley Sokari da Saviour Godwin da Dele Alampasu sai Musa Yahaya da Moses Simon.

Ana sa ran za’a fara horas da ‘yan wasan tawagar dake gida yau Litinin, ‘yan wasan wajen da aka kira kuwa zasu taho gida nan da sati biyu, wato kafin lokacin karawar kungiyar da kasar Congo.

A wani bangaren kuma Siasia ya kori ‘yan wasa har bakwai daga kungiyar matasan, biyo bayan kunen doki da sukayi a wasan su da Wikki Tourists ta Bauchi.

Siasia yace, “na baiwa ‘yan wasan lokaci domin su nuna min bajintar su, amma suka bani kunya kasancewar har yanzu ba su tabbatar min da cewar zasu iya ba, yanzu kuwa sun budewa wasu kofa na zuwa da nuna min in zasu iya.”

Ya kuma godewa ‘yan wasan kan taimakawar da sukayiwa kungiyar ga samin nasarorin ta a baya, amma yace yanzu dole mu ci gaba ba tare da su ba, idan kuma munga suna nuna kwazo a kungiyar su to zamu sake gayyato su.

‘Yan wasan da korar ta shafa kuwa sun hada da Sani Faisal da Lukmon Gilmore da Emmanuel Ammana da Tonbara Tiongoli da Freedom Omofonma da Uche Okeke da Gabriel Sunday.