Tsohon Mai horas da tawagar Kungiyar kwallon kafa Super Eagles, ta Najeriya, Samson Siasia, na daya daga cikin jerin sunayen Mutane takwas da aka jera za'a zaba a matsayin Mai horas da Kungiyar kwallon kafa ta kasar Rwanda.
Jerin sunayen sun hada da Winfried Schafer Paul Put, tsohon Kocin Burkina faso 2013, sai Georges Leekens, wanda ya ajiye aikinsa da Kasar Algeria, a watan da ya wuce Sakamakon rashin tabuka abin kirki a gasar AFCON 2017 Schafer Led, da ya taba rike Kungiyar Kamaru 2002.
Sauran sun Fito ne daga yankin turai irin su Jose Rui, Lopes Aguas, da Raoul Savoy, dan kasar Swiss, sai Peter James Butler, daga Ingila, daga karshe akwai dan kasar Jamus Antoine Hey.
Wadannan sune Wadanda suka haye daga cikin mutane hamsin da biyu da suka kai takardunsu don neman a daukesu aiki a matsayin masu horaswa na Kungiyar kwallon kafar kasar Rwanda.
Daga karshe hukumar zata fitar da mutum daya daga cikin mutane takwas da suka rage domin zama babban kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar Rwanda.
Kasar Rwanda, dai tana fama da rashin tsayayyen Mai horas da ‘yan wasan kwallon kafa na dindindin tun a watan Agustan Shekarar data gabata bayan ta kori kocinta Jenny Mckinstry.