Shugabar 'Yan Adawan Belarus Tana Hannun Jami'an Tsaro

Shugabar 'yan adawan Belarus, Maria Kolesnikova

Jami’an tsaron kan iyakar kasar Belarus sun ce, an tsare shugabar ‘yan adawar kasar Maria Kolesnikova da safiyar jiya Talata yayin da take kokarin tsallaka iyaka zuwa makwabciyar kasar Ukaraine.

Jami’an sunce Kolesnikova ta na tafiya ne da wasu mambobin kungiyar ‘yan adawa, Anton Rodnenkov da Ivan Kravtsov, wadanda dukansu suka yi nasarar shiga Ukraine.

Sai dai nan da nan ba a gane yanayin da ya sa mutanen suka tsinci kansu a iyakar ba.

Mataimakin ministan harkokin cikin gida Anton Gerashchenko, ya rubuta a shafin Facebook cewa, abin da ya faru ranar Talata ba tafiya bace ta radin kai, amma ya kira ta da abin da ya ce tafiya ce ta tilastawa.

Ranar Litinin ne kasashen Jamus da Birtaniya suka yi kira ga shugaban kasar Belarus Alexander Lukashenko, da ya bayyana wurin da Kolesnikova ta ke, bayan da rahotanni ke nuni da cewa, wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun kamata a birnin Minsk.

Kamfanin dillancin labaru na Reuters ya fitar da rahotan dake cewa kungiyar tarayyar Turai EU a takaice, na duba yiwuwar kakabawa wasu manyan jami’an Belarus 31 takunkumi, rahotan ya ambaci wasu jami’an diplomasiyar EU uku.