Daraktar Muryar Amurka Amanda Bennett da babbar mataimakiyarta Sandra Sugawara sun yi murabus daga aikinsu.
A cikin sanarwar da ta fitar ta ce, Micheal Pack, sabon shugaban hukumar USAGM da Muryar Amurka ke karkashinta, yana da damar da zai nada duk wanda ya ke so ya jagoranci ma’aikatar.
Bennett da Sugawara, baki dayansu tsoffin ‘yan jarida ne, kuma sun jagoranci Muryar Amurka tun shekarar 2016, inda suka fadada ayyukan labaran da hukumar mai zaman kanta ke yadawa a talabijin da radiyo kuma ta yanar gizo cikin yaruka 47 a fadin duniya.
Cikin wasikar ajiye aiki da su ka rubuta, Bennett da Sugawara sun fadawa daruruwan marubuta da editoci da dukkan ma’aikata cewa sun samar da sauyi cikin shekaru hudun da suka yi suna aiki.
Haka kuma, sun tabbatarwa da ma’aikatan Muryar Amurka cewa “babu wani abu da zai sauya akan aiki ko inda aka saka gaba, idan Mista Pack ya karbi ragamar shugabancin Muryar Amurka da ma hukumar USAGM baki daya."
Hakan na faruwa mako daya bayan da Micheal Pack ya fara aiki a matsayin sabon shugaban hukumar USAGM.