Shugabar Koriya Ta Kudu Tayi Wani Jawabin Gaggawa

Ba tare da yin amfani da kalmomin murabus ko tumbukewa ba, shugabar Koriya ta kudu Park Geun-hye ta bayyana niyyar sauka daga mukaminta a cikin lumana, muddin majalissar dokokin kasar ta bukaci tayi hakan.

A wani jawabin gaggawa da ta yi a kafar talabijin, Park ta ce “matakin da zata dauka nan gaba, ciki har da rage tsawon wa’adinta na mulki, zai dogara kan duk wani matakin da majalisar dokoki zata dauka.”

Ta kuma kara da bada abinda za a ce sharadu ne, ba tare da bada lokacin saukarta daga mukamin ba, tana mai cewa “zata bar kujerarta ta shugabar kasa bisa ga tsari da kuma shirin doka, bisa kuma ga matakan da jam’iyya mai mulki da ta ‘yan adawa zasu kirkiro don kawas da hargitsi da gibi a harkokin kasar, su kuma kafa wata gwamnatin cikin kwanciyar hankali.”

Shugabannin jam’iyyun adawa sun mayar da murtanin rashin tabbas akan jawabin shugabar. Wasu na gani cewa wannan wata dabara ce ta jinkirta shirin tsige ta daga mukamin da kuma kara samun goyon baya daga jam’iyyarta ta Saenuri party.