Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Dan Asalin Somalia Ya Taka Mutane da Mota Ya Kuma Yi Suka da Wuka A Jihar Ohio Nan Amurka


Motar da dan asalin Somalian yayi anfani da ita yana taka mutane a jami'ar Ohio
Motar da dan asalin Somalian yayi anfani da ita yana taka mutane a jami'ar Ohio

‘Yansandan jihar Ohio dake nan Amurka sun bindige kuma sun kashe wani matashi dan kasar Somalia da ya tuka motarsa zuwa cikin Jami’ar Jihar Ohio din, ya tattaka mutane da dama sannan kuma ya fito motar ya dinga kai hari akan wasu da wuka, yana ta sukansu, inda kuma karshenta ya raunana mutane 11.

Babbar sufeton ‘yansandan birnin Columbus, Kim Jacobs tace suna kallon wannan farmaki a matsayin harin ta’addanci.

Hukumomin jami’ar ta Ohio sun bada sunan wanda ya kai harin da cewa ana kiran shi Abdul Razak Ali Artan, wanda ashe ma dalibin makarantar da ya kaiwa hari ne.

Mazauna garin dai sun gayawa sashen Somaliyanci na VOA cewa matashi, mai kamar shekaru 20, dan asalin Somalia ne.

Ta wani gefen irin wanan kuma...Baturen nan farar fata da ya kashe mutane bakaken fata guda 9 yayinda suke cikin wata coci a birnin Charleston dake jihar Carolina ta Kudu, ya samu iznin hukuma na ya wakilci kansa a matsayin lauyan kansa a shara’a da ake mishi na kisan kawunan da yayi.

A jiya Litinin ne wani alkali ya baiwa Dylann Roof iznin ya shirya zama lauyan kansa a shara’ar da za’ayi mishi inda zai fuskanci zargin aikata lafukka 33 wadanda suka hada da wadanda, idan aka same shi da laifin aikata su, ana iya yanke mishi hukuncin kisa.

Kudurin wannan Baturen na ya wakillci kansa a matsayin lauyan kansa ya biyo ne bayan cacar bakin da aka share wattani ana yi da shi bayanda yayi tayin cewa ya yarda ya amsa laifukkan da ake zarginsa da aikatawa idan hukumomi sun yarda su yanke mishi hukuncin daurin rai da rai maimakon hukuncin kisa, abinda hukumomin suka ki yarda da hakan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG