Shugabar huldar siyasar kasashen waje na kungiyar Federica Mogherini ya bukaci da Ministocin na Turai da su daina cin diddigen maganar rarraba ‘yan gudun hijirar a Turai.
Majalisar dokokin kasar Hungary ta umarci sojojin kasar da ta yi amfani da makamin da ba zai kai ga halaka ba wajen hana shigar ‘yan gudun hijira cikin kasar ba bisa ka’ida ba.
Kasar dai tuni da datse kan iyakarta da Serbia ta hanyar sa shingen waya mai kaifi. Sojojin na Hungary za su iya amfani da harsashin roba ko barkonon tsohuwa da makamantansu.
Suna ma iya caje gida-gida don farautar bakin hauren ba bisa ka’ida ba. Sauran kasashen tarayyar Turai sun yi tir da yadda Hungary ke wa ‘yan gudun hijirar.
Inda suka cewa kasar na amfanin da dabarun karfa-karfa irin wadanda ‘yan Nazi suka yi amfani da shi a baya.