A Sudan ta Kudu, shugaba Salva Kiir,mataimakin shugaban kasa na farko kuma tsohon madugun 'yan tawaye Riek Machar, da kuma mataimakin shugaban kasa James Wani Igga, sun gana cikin wannan mako domin tattaunawa kan sauran batutuwa da suke hana ruwa wajen aiwatar da yarjejeniyar sulhu da suka amince da ita.
WASHINGTON DC —
Mukakkadashin sakatare a kwamitin kasa mai kula da yada labarai William Ezekiel, yace shugabannin uku sun tattauna kan batun kwance damara a Juba, batun wurare domin dakaru daga bangaren adawa a sassan kasar uku, da kuma takaddama kan jihohi 28 da shugaba Kiir ya kirkiro a radin kansa bara. Ezekiel yace shugabannin zasu kirkiro da kwamiti da zai yi nazarin jihohin da ake kuduri da duk sassan suka yarda.
Ana sa ran kwamitin zai mika rahotonsa cikin kwanaki 30 da shawarwarinsa kan yawan jihohi da kuma iyakokinsu.
Kwamitin yana kunshe da wakilia 15, ciki harda kasashen duniya uku Amurka, da Ingila da kuma Norway. Kasashen Tanzania da Afirka Ta Kudu suma zasu bada wakilai 2.