Shugabannin Siyasar Jahar Borno na Zargin Junan su da Hannu a Harin Maiduguri

Hoton da Wakilin Sashen Hausa Haruna Dauda Biu ya aiko daga Maiduguri bayan harin da aka kai ranar talata 14 ga watan janairu

Cece-ku-ce ya barke tsakanin bangaren tsohon gwamnan jahar ta Borno Ali Modu Sharif da kuma na gwamna mai ci yanzu Kashim Shettima
Cece-kuce da zarge-zargen juna sun biyo bayan harin bom din da aka kai unguwar post office a tsakiyar birnin Maiduguri, jahar Borno. Kwana daya bayan harin an tabbatar da mutuwar mutane arba'in da uku da suka hada da maza da mata da yara, kuma likitoci sun ce yawan mace-macen na iya karuwa saboda wasu na ta mutuwa sanadiyar raunukan da suka samu:

Your browser doesn’t support HTML5

Zargin juna da cece-ku-ce tsakanin manyan 'yan siyasar jahar Borno - 2:57


Wakilin Sashen Hausa a jahar Borno, Haruna Dauda Biu ne ya aiko da rahoton dga birnin Maiduguri.